Wata sabuwa: Buhari ba zai samu tikitin takara tazarce a APC kai tsaye ba

Wata sabuwa: Buhari ba zai samu tikitin takara tazarce a APC kai tsaye ba

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana cewa duk da bayyana ra'ayin sa na sake tsayawa takara da yaye a jam'iyya, ko kusa jam'iyyar ba ta da niyyar ba shugaban kasar tikitin ta kai tsaye ba tare da zabukan fitar da gwani ba.

Babban jami'in watsa labaran jam'iyyar ne dai Malam Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan lokacin da yake fira da manema labarai a babban ofishin jam'iiyar na kasa dake a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Wata sabuwa: Buhari ba zai samu tikitin takara tazarce a APC kai tsaye ba

Wata sabuwa: Buhari ba zai samu tikitin takara tazarce a APC kai tsaye ba

KU KARANTA: Allah ya hana Buhari ikon sake yin takara - Matar Obasanjo

Legit.ng ta samu cewa ana rade-raden cewa wasu 'yan siyasa kamar su Sanata Bukola Saraki da Sanata kwankwaso har ma da Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal dai suna cikin masu sha'awar takarar.

A wani labarin kuma, Tshohuwar matar tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar Cif Olushegun Obasanjo mai suna Taiwo ta bayyana ra'ayin ta na cewa ko kusa ba ta fatan shugaban kasar Najeriya na yanzu ya sake tsayawa takara a 2019.

Uwar gida Taiwo din dai ta bayyana ra'ayin nata ne a yayin wata firar da ta yi da majiyar mu a karshen sati inda ta ayyana cewa ita yanzu tana ba shugaba Buhari shawara da ya tattara kayan sa ya koma jihar sa ta Katsina.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel