Dalilan Ministar kudi da take ta korar wasu manyan daraktoci

Dalilan Ministar kudi da take ta korar wasu manyan daraktoci

- An sauke wasu manyan daraktocin ne saboda zargin rashawa

- Wasunsu kuma an canja musu mazaunai ko kuma aika su wani aikin daban

- Yawancinsu sun karyata wannan zargi, inda suke cewa kawai sharri ne da shafa kashin kaji

Dalilan Ministar kudi da take ta korar wasu manyan daraktoci
Dalilan Ministar kudi da take ta korar wasu manyan daraktoci

Dalilai sun bayyana a daren juma'a abinda yasa ministar kudi, Kemi Adeosun, ta saka sandar ikon ta, ta tumbuke shugaban hukumar tsaro da musaya, Abdul Zubair da wasu jiga jigan hukumar daga kujerunsu.

A ranar juma'a aka zabi Mary Uduk don ta maye gurbin Mista Zubair wanda aka maida shi bangaren External Relations.

Mai magana da yawun ministan, Oluyinka Akintunde ya fada sauran manyan hukumar da aka tumbuke. Sun hada da Reginald Karawusa wanda yake matsayin zababben kwamishinan dokoki da tabbatar dasu.

Isiyaku Tilde mai matsayin zababben kwamishina na aiyuka da Henry Adekunle mai matsayin zababben kwamishina aiyukan hadin guiwa.

Daga majiya mai karfi PREMIUM TIMES taji a ranar juma'a cewa an sanar da cigaban ne biyo bayan hargitsin da ya faru a ranar laraba bayan yanke hukuncin dage dakatar da siye da siyarwa na hannun jarin Oando PLC.

An dakatarwar siye da siyarwar hannayen jarin kamfanin a 23,October, 2017 sakamakon zargin da aka yi na juyarda yanayin mallaka na kamfanin.

Ma'aikatar Kudi ta Najeriya tace an dauke zancen dakatarwan ne a ranar alhamis bayan samun wasikar SEC mai kwanan wata 9 ga Afirilu. Awoyi bayan sanarwar dage dakatarwan ne aka samu umarnin da ya ci Karo da hakan. Wannan shima an janye shi a yammacin ranar.

Majiyar da tace a sakaya sunan ta domin ba a bada damar zantawa akan maganar ba tace hargitsin dai ya matukar kunyata Gwamnatin.

DUBA WANNAN: Mun dakatar da sulhu da Boko Haram

Amma bayanin da kuma bada hakurin ya iso a makare ne bayan an hukunta jami'an.

Mrs Adeosun ta bukaci bayani daga hukumar karkashin jagorancin Abdul Zubair. Majiyar tace Mr Zubair dai yace bai San komai ba akan umarnin.

Ya dorawa wani mataimakin shi laifin bada umarnin ba tare da sanin shi ba. Rashin gamsuwar ministan ne ya jawo canza musu bangarori domin kare Gwamnatin da wata Jin kunyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel