Sai yanzu Buhari ya yarda cewa akwai kudaden da Abacha ya kwasa

Sai yanzu Buhari ya yarda cewa akwai kudaden da Abacha ya kwasa

- An dawo da kudaden da Abachan ya kai Turai a makon jiya

- Har yanzu biliyoyin kudaden suna can a Turai

- Abacha ya ajje kudin ne ko don kansa ko don Najeriya

Sai yanzu Nuhari ya yarda cewa akwai kudaden da Abacha ya kwasa
Sai yanzu Nuhari ya yarda cewa akwai kudaden da Abacha ya kwasa

Bayan da Najeriya ta sake karbar wasu karin kudaden da sun kai dala miliyan fiye da dari ukku, shekaru 20 bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha, kamar dai shugaba Buhari ya yarda kenan akwai kudaden da ake sa rai biliyoyi ne na daloli da Janar din ya kwashe.

Kudaden dai, ga masoya Abachan, suna cewa ne ya ajje ssu ne domin ko-ta-kwana, saboda yawan takunkumai da aka sanya wa kasar nan a lokacin juyin mulkinsa.

Amma da yake har yanzu wadanda ya daddaure ke mulki, sai ake cewa wai sace su yayi, domin ya dinga rantawa kasar kudi lokuta-lokuta ya mulke ta na din-dindin.

DUBA WANNAN: Malabu: Minista Adoke bayyi laifin komai ba

Shugaba Buhari dai, a shekarar 2008, ya ce babu wasu kudi da Abacha ya diba lokacin mulkinsa, domin babu wata hujja da ta nuna hakan.

Amma sai gashi yau shi da kansa yake karbar biliyoyin kudaden da aka sakar wa kasar nan, bayan da suka jujjuya suka baiwa turawan Switzerland uwar riba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel