Ta zarcen Buhari: Jiga-jigan jam'iyyar APC na ta shirye-shiryen ficewa

Ta zarcen Buhari: Jiga-jigan jam'iyyar APC na ta shirye-shiryen ficewa

Biyo bayan ayyana kudurin sake tsayawa takarar tazarce da shugaba Muhammadu Buhari yayi a satin da ya gabata yayin taron masu ruwa-da-tsaki na jam'iyyar APC mai mulki, alamu na ta nuna yiwuwar ficewar wasu jiga-jigan jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyun domin samun tikitin takara a 2019.

Duk da dai har yanzu ba'a fallasa sunayen masu neman ficewa daga jam'iyyar ba, amma dai jam'iyyun da ake tunanin za su yi sabbin baki sun hada da Social Democratic Party (SDP), Labour Party (LP), Accord Party (AP) da kuma hadakar nan ta tsohon shugaba Obasanjo ta Coalition for Nigeria Movement (CNM).

Ta zarcen Buhari: Jiga-jigan jam'iyyar APC na ta shirye-shiryen ficewa

Ta zarcen Buhari: Jiga-jigan jam'iyyar APC na ta shirye-shiryen ficewa

KU KARANTA: Ko wacece tsohuwar matar Dangote?

Legit.ng ta samu cewa cikin wadanda ake ta rade-raden za su fice daga jam'iyyar APC sun hada da gwamnoni, Sanatoci da ma 'yan majalisar wakillai da dama.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa shugaba Buhari ya ayyana yana so ya sake tsayawa takara ne a ranar litinin din da ta gabata jim kadan kafin ficewar sa kasar zuwa birnin Landan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel