Ya yi laifi da gan-gan domin a kai shi kurkuku yayi fara wata sana'a mai ban mamaki

Ya yi laifi da gan-gan domin a kai shi kurkuku yayi fara wata sana'a mai ban mamaki

Wani gawurtacen barawo mazaunin Shanghai mai suna Wanng, mai shekaru 45 ya aikata laifin sata a cikin kwanakin nan kawai don a kai shi fursuna ya sami damar shiga wata kungiyar masu rawa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kotu ta yanke wa Wanng hukuncin watanni 10 a gidan yari tare da tarar $320 bayan an same shi da laifin satar wayoyin salula a asibitin birnin Jiading. Ya amsa dukkan laifin da aka karanta masa inda yace ba talauci bane yasa yayi satar.

Wani yayi sata da gangan saboda a kai shi fursuna ya fara wata sana'a

Wani yayi sata da gangan saboda a kai shi fursuna ya fara wata sana'a

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa har yanzu ba'a ceto 'yan matan Chibok ba - Buhari

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Wanng ya shaida wa yan sanda cewa ya aikata satar ne don yana ganin itace hanya mafi sauki da yake da ita na shiga kungiyar rawa na gidan fursunan Shanghai Tilanqiao wadda ta lashe kyaututtuka da dama kuma sunyi wasanni sama da 5,700.

"Ina bukatar damar da zan nuna bajinta ta na waka,"

"Kungiyar Tilanqiao zata bani wannan damar tunda suna wasanni a fursunoni da dama. Da zarar isa fursuna, zan samu damar cika buri na. Ba zan sake maimaita kurakuren da nayi a baya ba. Ba zan maimaita ba," inji Wanng.

Yu Zhong, jami'in da ya shigar da kara a kotun Jiading, ya ce tabbas abin mamaki ne yadda Wanng ya saukakawa yan sanda bincike da kuma kamo shi. Yace Wanng ya bayar da sunansa na gaskiya daya shigo asibitin kuma ya bayyana fuskarsa sosai yayinda ya fuskanci kyamara.

Barayi da muka saba kamawa basu son a gano su amma shi Wanng yayi duk mai yiwuwa ne don ya kama shi kuma ayi saurin yanke masa hukunci zuwa gidan yari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel