Mutan garinsu Sanata Omo-Agege sun maka majalisa a kotu saboda hukuncin da akayi masa

Mutan garinsu Sanata Omo-Agege sun maka majalisa a kotu saboda hukuncin da akayi masa

Mambobin kabilar Urhobo da ke jihar Delta sun maka majalisar dattawa a kotu saboda dakatar da Sanata mai wakiltan yankin Delta ta tsakiya, Sanata Ovie Omo-Agege bisa wasu kalamai da ya fada game da canja jadawalin zaben 2019 da majalisar ke yunkurin yi.

Kungiyar ta shigar da kara a babban kotun Abuja inda suke bukatan a janye dakatarwar da akayi wa Sanatan saboda yin hakan tauye hakkin wakilcin al'ummar yankin ne, wanda hakan baya yiwuwa kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya nuna.

Mutan garinsu Sanata Omo-Agege sun maka majalisa a kotu saboda hukuncin da akayi masa

Mutan garinsu Sanata Omo-Agege sun maka majalisa a kotu saboda hukuncin da akayi masa

An dakatar da Sanata Omo-Agege na a ranar Alhamis da ta gabata har na tsawon kwanaki 90 bayan tattaunawa mai tsawo a majalisar saboda kalaman da ya furta game da yiwa sashi na 25 na dokar zabe.

DUBA WANNAN: Asiri ya tonu: Dakurun soji sun kama wasu da ke da hannu cikin kashe-kashen jihar Taraba

A kwaskwarimar da majalisa ke kokarin yiwa dokar zaben, ana sa ran za'a fara gudanar da zabukan yan majalisar jihohi da tarayya kana ayi na gwamnoni sai zaben shugaban kasa ya biyo baya.

Mr. Omo-Agege yayi Allah wadai da gyaran dokar da ake kokarin yi a majalisar wanda yan majalisa 36 cikin 360 ne kawai suke nan a majalisar wakilai lokacin da aka karanto kudirin gyaran dokar a majalisar.

Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi ne ya gabatar da batun gaban majalisar dattawa kuma daga bisani aka mika ta zuwa ka kwamitin da'a inda daga baya sukayi bincike kuma suka bayar da shawarar dakatar da sanatan na kwanaki 181 amma majalisar sukayi sassauci zuwa kwanaki 90.

Kwamitin tace an dauki matakin hukuncin kan Mr. Omo-Agege ne saboda shigar da kara kotu da yayi bayan ya nemi afuwar majalisar.

Hakazalika, wani lauya mai kare hakkin bil adama, Frank Tietie ya yi tir da dakatar da sanatan inda shima yayi barazanar zai shigar da kara kotu idan majalisar bat janye dakatarwar da tayi wa Sanatan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel