An kama manyan makamai a jihar Filato, da kuma masu fyade har 24

An kama manyan makamai a jihar Filato, da kuma masu fyade har 24

- Hukumar Yan sanda reshen jihar Filato tayi nasarar kwato makamai masu yawa a hannun batagari a jihar

- Hukumar ta kuma koka kan yadda ake samun karuwar masu aikata laifin fyade a jihar

- Kwamishinan Yan sandan jihar ya shawarci iyayen yara su sanya ido akan yaransu musamman mata saboda karesu daga miyagu

Hukumar Yan sanda reshen jihar Filato ta sanar da cewa ta kwato bindigogi da alburusai guda 1,097 daga hannun bata gari a jihar. Cikin makaman da aka kwato sun hada da bindigogi guda 171, alburussai guda 795 da kuma wasu kwallayen alburusan guda 131.

Hukumar kuma ta koka kan yadda ake samun karuwar laifukan fyade a jihar, inda tace an kama masu fyade 19 zuwa 24 a cikin watan Fabrairu da ta gabata kuma dukkan wandanda ake tuhuma an gurfanar dasu a gaban kuliya.

'Yan sanda sun kwato makamai 1,097 tare da kama masu fyade 24 a jihar Filato

'Yan sanda sun kwato makamai 1,097 tare da kama masu fyade 24 a jihar Filato

DUBA WANNAN: Mutan garinsu Sanata Omo-Agege sun maka majalisa a kotu saboda hukuncin da akayi masa

Kwamishinan Yan sanda na jihar, Undie Adie ya bayar da wannan sanarwan yayin da yake gabatar da wasu gungun barayin motoci da babura da ake tuhuma da laifin kisa baya ga satan da suka saba aikatawa.

Yace hukumar Yan sanda a jihar ta dukufa wajen kawar da makamai daga hannun al'umma kamar yadda Sifeta Janar na hukumar ya bayar da umurni inda yace a halin yanzu an fara samun nasara a cikin aikin.

"Abin takaici ne yadda ake samun karuwar masu aikata laifin fyade a jihar ta Filoto. A ranar 30 ga watan Janairun 2018, hukumar ta gabatar da wasu mutane uku da sukayi fyade ga wata yarinya mai shekaru 14 a Unguwan Rogo da ke Jos, tuni an riga an gurfanar dasu a kotu," inji shi.

Adie ya kuma shawarci iyayen yara sun snya idanu kan yayansu musamman mata don kare su daga fadawa hannun bata garin mazaje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel