Dalilin da yasa har yanzu ba'a ceto 'yan matan Chibok ba - Buhari

Dalilin da yasa har yanzu ba'a ceto 'yan matan Chibok ba - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari yace gwamnatin sa bata manta da 'yan matan Chibok ba

- Shugaban yace ceto an samu jinkiri wajen ceto yan matan ne saboda rashin jituwa da aka samu tsakanin yan Boko Haram da ke rike dasu

- Shugaban kasar ya tabbatar wa yan Najeriya cewa gwamnatinsa zata cigaba da kokarin ganin cewa an ceto yan matan

A jiya Juma'a ne shugaba Muhammadu Buhari yace an samu tangarda ne cikin tattaunwar da akeyi tsakanin gwamnatin tarayya da yan kungiyar na Boko Haram shiyasa har yanzu ba'a sako yan matan makarantar sakandire na Chibok da aka sace shekaru hudu da suka shude ba.

Dalilin da yasa har yanzu ba'a ceto 'yan matan Chibok ba - Buhari

Dalilin da yasa har yanzu ba'a ceto 'yan matan Chibok ba - Buhari

Shugaban kasar yace tangardar ya afku ne saboda rashin jituwa tsakanin 'yan Boko Haram din da suka sace 'yan matan. Shugaban kasar ya bayar da wannan sanarwan ta bakin hadiminsa na musamman a fanin yadda labarai, Garba Shehu.

DUBA WANNAN: Laifin kisa: An yankewa wani saja hukuncin kisa ta hanyar rataya

Wasu daga cikin kalamansa, "Muna sane da cewa an dauki lokaci mai tsawo ba tare da ceto yan matan ba kuma abin yana matukar damun mu amma tabbas gwamnati nayi iya kokarinta don ganin an ceto yan matan daga wandanda suka sace su.

"Sai dai an samu tangarda cikin tattaunawar da gwamnati keyi da yan ta'addan saboda rashin jituwa tsakanin wadanda ke rike da yan matan wanda hakan yasa abin ke daukan lokaci.

"Duk da hakan, gwamnatin ba zatayi kasa a gwiwa ba. Zamu cigaba da kokarin kuma muna rokon iyayen su kara juriya kuma kar su taba tunanin cewa gwamnati ta manta da batun yan matan, domin bamu cire rai a kansu ba."

A wata rahoton kuma, Asusun yara na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa sama da yara 1000 yan kungiyar Boko Haram suka sace a yankin na arewa maso gabashin Najeriya tun 2013 ciki har da yan matan Chibok 276 da aka sace a ranar 14 ga watan Afrilun 2014.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel