Wani hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 4 da raunata 19 a jihar Kano

Wani hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 4 da raunata 19 a jihar Kano

Mutane hudu ne suka riga mu gidan gaskiya tare da raunatar wasu mutane 19 a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kan babbar hanyar zuwa garin Bauchi daura da kauyen Dogon Danmarke dake karamar hukumar Wudi ta jihar Kano.

Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar, Alhaji Sa'idu Muhammad, shine ya tabbatar da wannan lamari da ya afku da misalin karfe 10.44 na safiyar ranar Juma'ar da ta gabaya yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa.

Wannan hatsari ya afku ne a yayin da wasu motoci uku suka gwabza da suka hadar da; Toyota Hummer mai lambar SA 297 GME; Golf mai lambar SSP 134 ES da kuma wata motar kirar Sharon mai lambar SA 158 PAT.

Wani hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 4 da raunata 19 a jihar Kano

Wani hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 4 da raunata 19 a jihar Kano

Alhaji Sa'idu ya bayyana cewa, duk da cewar tsautsayi ba ya wuce ranar sa wannan hatsari dai ya afku a sakamakon gudu da ya sabawa ka'ida da sakamakon sa ya janyo wa mutane 23 kaffara.

KARANTA KUMA: Fashewar Bam ta kashe mutane 5 yayin wasan kwallon kafa a kasar Somalia

Kakakin ya kara da cewa, an garzaya da wadanda hatsarin ya shafa zuwa babban asibitin garin Wudil, inda Likitoci suka tabbatar da mutuwar 4 nan take yayin da 19 kuma ke karbar magani.

Ya kuma nemi masu ababen hawa da su guji sabawa dokokin tuki musamman akan manyan hanyoyi domin rage afkuwar hadurra da zai kare rayuka da asarar dukiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel