Yanzu Yanzu: Fashin Offa – Yan sanda sun saki sunayen mutane 12 da aka kama

Yanzu Yanzu: Fashin Offa – Yan sanda sun saki sunayen mutane 12 da aka kama

A ranar Juma’a, 13 ga watan Afrilu, rundunar yan sanda Najeriya sun bayyana sunayen mutane 12 da aka kama da hanu a mummunan fashin da akayi a Offa, jihar Kwara.

Yan fashin sun kai farmaki garin a ranar 5 ga watan Afrilu inda suka kashe mutane 17 sannan suka kai hari bankuna biyar. Yan sanda takwas a hukumar Owode, Offa na daga cikin wadanda aka kashe a harin, sannan kuma yan fashin sun tafi da makaman yan sanda.

Yan sandan sun kama mutane bakwai cikin kwanakin biyun farko da kai harin, sannan kuma daga baya suka sake wasu hare-haren.

Yanzu Yanzu: Fashin Offa – Yan sanda sun saki sunayen mutane 12 da aka kama

Yanzu Yanzu: Fashin Offa – Yan sanda sun saki sunayen mutane 12 da aka kama

KU KARANTA KUMA: Shugaban ‘yan kato da gora yace an gana masa azaba akan yayiwa Shehu Sani Sharri

Ga sunayen yan fashin:

1. Adegoke Shogo shekaru 29 – An kama shi a Offa

2. Kayode Opadokun shekaru 35 – An kama shi a Offa

3. Kazeem Abdulrasheed shekaru 36 – An kama shi a Offa

4. Azeez Abdullahi shekaru 27 – An kama shi a Offa

5. Alexander Reuben shekaru 39 – An kama shi a ranar ga watan Afrilu, 2018 a Lagos

6. Jimoh Isa shekaru 28 – Arrested on the 11th April, 2018 in Lagos

7. Azeez Salawudeen shekaru 20 – An kama shi a Offa dauke da waya da sim din wanda aka kashe

8. Adewale Popoola shekaru 22 – An kama shi a Offa dauke da waya da sim din wanda aka kashe

9. Adetoyese Muftau shekaru 23 – An kama shi a Ibadan,jihar Oyo

10. Aminu Ibrahim shekaru 18 – An kama shi a Ilorin

11. Richard Buba shekaru Terry 23 – An kama shi a Ilorin

12. Peter Jaba Kuunfa shekaru 25 – An kama shi a Ilorin

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel