Yanzu Yanzu: Yar wasan tsere ta Najeriya mai shekaru 20 ta kafa tarihi

Yanzu Yanzu: Yar wasan tsere ta Najeriya mai shekaru 20 ta kafa tarihi

- ‘Yan wa an tsere ta Najeriya mai shekaru 20 Oluwatobiloba Amusan ta kafa tarihi inda ta zama ‘yar Najeriya ta farko dataci sarkar zinari a tseren mata na 100m wasannin commonwealth

- Oluwatobiloba Amusan ta samu wannan nasara ne ranar Juma’a filin wasanni na Carrara a Gold Coast, na kasar Australia

- ‘Yar wasannin wadda yanzu itace ta zama ta uku cikin wadanda suka samu irin wannan nasara bayan Modupe Oshikoya wadda taci azurfa a shekarar 1974 da Angela Atiede wadda itama taci azurfa a shekarar 2002

‘Yan wasanni ta Najeriya mai shekaru 20 Oluwatobiloba Amusan ta kafa tarihi inda ta zama ‘yar Najeriya ta farko dataci sarkar zinari a tseren mata na 100m wasannin commonwealth.

Oluwatobiloba Amusan ta samu wannan nasara ne ranar Juma’a filin wasanni na Carrara a Gold Coast, na kasar Australia. Tayi nasara ne inda tayi gudun cikin dakika 12.68, ta samu nasarar.

Yanzu Yanzu: Yar wasan tsere ta Najeriya mai shekaru 20 ta kafa tarihi

Yanzu Yanzu: Yar wasan tsere ta Najeriya mai shekaru 20 ta kafa tarihi

‘Yar wasannin wadda yanzu itace ta zama ta uku cikin wadanda suka samu irin wannan nasara bayan Modupe Oshikoya wadda taci azurfa a shekarar 1974 da Angela Atiede wadda itama taci azurfa a shekarar 2002.

KU KARANTA KUMA: Shugaban ‘yan kato da gora yace an gana masa azaba akan yayiwa Shehu Sani Sharri

Danielle Williams ‘ya kasar Jamaica itace ta zamo ta biyu, inda taci azurfa, bayan data gama nata gudun cikin dakika 12.78. Yanique Thompson, itama ‘yar kasar Jamaica, taci karamar azurfa inda ta gama nata gudun cikin dakika 12.97. Nasarar Amusa ya zama zinari na takwas da Najeriya ta samu a wasannin commonwealth.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel