An saki Adeyanju yayinda ‘Yan Sanda suka hana zanga-zanga a Unity Fountain

An saki Adeyanju yayinda ‘Yan Sanda suka hana zanga-zanga a Unity Fountain

- Hukumar ‘Yan Sanda ta birnin tarayya ta sallami masanin hakkin dan adam Deji Adeyanju wanda aka kama a unity fountain a birnin tarayya bisa zargin hana zaman lafiya

- An kama Adeyanju lokacin zanga-zangar kungiyar ‘Yan Shi’a ta INM, wanda ke zanga-zanga don a saki shugabansu Ibraheem El-Zakzaky

- Hukumar ‘Yan Sandan ta sakeshi ne bayan da Charles Oputa (Charly Boy) shugaban kungiyar OurMumuDonDo, yaje sun gana da kwamishinan ‘Yan Sandan Sadiq Abubakar Bello don a sakeshi

Hukumar ‘Yan Sanda ta birnin tarayya ta sallami masanin hakkin dan adam Deji Adeyanju wanda aka kama a unity fountain a birnin tarayya bisa zargin hana zaman lafiya.

An kama Adeyanju lokacin zanga-zangar kungiyar ‘Yan Shi’a ta INM, wanda ke zanga-zanga don a saki shugabansu Ibraheem El-Zakzaky.

Hukumar ‘Yan Sandan ta sakeshi ne bayan da Charles Oputa (Charly Boy) shugaban kungiyar OurMumuDonDo, yaje sun gana da kwamishinan ‘Yan Sandan Sadiq Abubakar Bello don a sakeshi.

An saki Adeyanju yayinda ‘Yan Sanda suka hana zanga-zanga a Unity Fountain

An saki Adeyanju yayinda ‘Yan Sanda suka hana zanga-zanga a Unity Fountain

Kwamishinan yace babu wasu ‘yan kungiya da zasu kara gudanar da zanga-zanga a fountain.

KU KARANTAKUMA: Shugaban ‘yan kato da gora yace an gana masa azaba akan yayiwa Shehu Sani Sharri

Kungiyar masu goyon bayan Buhari a kafar sadarwa ta bukaci a hukunta Adeyanju a hukuntashi bisa laifin da ya aikata na hana mutane zama lafiya, ciyaman na kungiyar Austin Braimoh ya bayyana haka da sakataren kungiyar Cassidy Madueke

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel