Kotu ta bayar da wanda ake zargin yana satar mutane beli akan N500,000

Kotu ta bayar da wanda ake zargin yana satar mutane beli akan N500,000

- Kotun Ile-Ife wadda ke Osun ta bayar da wanda ake zargi da satar mutane Moshood Akewusola, beli akan kudi N500,000

- Alkaliyar kotun Adejumoke Ademola-Olowolagba, ce ta bayar dashi belin tare da mutane biyu wadanda zasu kawo Akewusola duk sadda kotu ta nemeshi

- Ta kuma bukaci daya daga cikin wadanda zasu tsaya masa din ya kasance ma’aikacin kotun ne sannan kuma dayan ya kasance ma’aikacin gwamnati wanda matsayinsa ya kai mataki na 8

Kotun Ile-Ife wadda ke Osun a ranar Juma’a ta bayar da wanda ake zargi da satar mutane Moshood Akewusola, mai shekaru 43, beli akan kudi N500,000.

Alkaliyar kotun Adejumoke Ademola-Olowolagba, ce ta bayar dashi belin tare da mutane biyu wadanda zasu kawo Akewusola duk sadda kotu ta nemeshi.

Ta kuma bukaci daya daga cikin wadanda zasu tsaya masa din ya kasance ma’aikacin kotun ne sannan kuma dayan ya kasance ma’aikacin gwamnati wanda matsayinsa ya kai mataki na 8.

Kafin nan mai gabatar da kara Speto Sunday Osanyintuyi, ya fadawa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 4 ga watan Afirilu da misalign karfe 7:30 na safe, a Ojoyin Street, Ile-Ife. Inda ya baiwa wani Abdulmaliq Ajala ruwan leda da magani a ciki dan yasha hankalinsa ya dauke ya sace shi.

KU KARANTA KUMA: Shugaban ‘yan kato da gora yace an gana masa azaba akan yayiwa Shehu Sani Sharri

Laifin wanda ya sabawa sashe 508 da 509 na dokar ta jihar Osun, ta 2002.

Duk da bai amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa ba, amma lauyansa Mista Samuel Obi, ya bukaci kotun da ta bayar dashi beli da tabbacin cewa bazai tsallake sharuddan belin ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel