Anyi babban kamu: Manyan Boko Haram 8 sunzo hannu

Anyi babban kamu: Manyan Boko Haram 8 sunzo hannu

Hukumar tsaro na NSCDC ta bayar da sanarwa damke wasu manyan yan kungiyar Boko Haram guda takwas da suka tsere daga Borno.

Sanarwar da ta fito daga bakin Kakakin hukumar, Emmanuel Okeh, a yau Juma'a ta kuma ce hukumar sun kama sama da mutane 100 da ke bannata kayan gwamnati. Okey yace a halin yanzu an gurfanar da masu bannata kayan gwamnatin a kotu.

Anyi babban kamu: Manyan Boko Haram 8 sunzo hannu

Anyi babban kamu: Manyan Boko Haram 8 sunzo hannu

DUBA WANNAN: Masana sunyi gargadi kan illolin amfani da wayyar salula da daddare ga dalibai

Okeh yace babban kwamandan hukumar, Abdullahi Gana, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin daliban cibiyar dabarun tsaro 'Natonal Insititute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) Kuru da suka ziyarci shi a hedkwatar hukumar a Abuja karkashin jagorancin AVM Humphery Okpala.

Gana ya bayyanawa tawagar cewa nasororin da hukumar ke samu yana da nasaba da hadin gwiwar da sukeyi tare da sauran hukumomin tsaro musamman yan jami'an tsaro JTF wanda ke taimaka musu da bayyanai masu amfani.

Yace irin wannan hadin gwiwar tayi aiki a arewa maso gabashin Najeriya kuma yana kyautata zaton zatayi aiki a sauran yankunan kasar nan wajen kawar da ayyukan batagari.

AVM Okpala ya shaida wa shugaban NSCDC cewa sun kawo ziyarar ne don su san matsayar hukumar kan batun nemo hanyoyin da al'umma zasu samar wa kansu kariya kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari ya umurci su da gudanar da bincike akai.

"Shugaban kasa ya daura wa hukumar nauyin gudanar da bincike kan hanyoyin da za'a magance matsalolin rashin tsaro da ke adabar wasu sassan kasar nan kuma su kai masa rahoton abin da suka gano," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel