Yanzu Yanzu: Gwamnan Jihar Abia Ikpeazu ya tsallake rijiya da baya

Yanzu Yanzu: Gwamnan Jihar Abia Ikpeazu ya tsallake rijiya da baya

- Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya tsallake kora daga daga hannun babban lauya, Friday Nwosu, wanda ya nemi a daina daukarsa a matsayin gwamnan jihar Abia

- Kotun koli ta kori karar wadda Nwosu dan jam’iyyar PDP ya shigar game da gwamnan, ta danne hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke

- Lauyan ya shigar da karar ne cewa Ikpeazu yayi karya a cikin form dinsa da ya gabatarwa hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC

Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya tsallake kora daga daga hannun babban lauya, Friday Nwosu, wanda ya nemi a daina daukarsa a matsayin gwamnan jihar Abia.

Kotun koli ta kori karar wadda Nwosu dan jam’iyyar PDP ya shigar game da gwamnan, ta danne hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Ikpeazu

Gwamnan Jihar Abia Ikpeazu ya tsallake rijiya da baya

Lauyan ya shigar da karar ne cewa Ikpeazu yayi karya a cikin form dinsa da ya gabatarwa hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

KU KARANTA KUMA: Shugaban ‘yan kato da gora yace an gana masa azaba akan yayiwa Shehu Sani Sharri

Nwosu tsohon dan takarar gwamnan ne a jihar ta Abia, a zaben Primary na jam’iyyar PDP a shekarar 2014 tare da Ikpeazu. Yayi ikirarin cewa Ikpeazu ya bada bayanin karya da kuma takardun haraji na karya da ya gabatarwa jam’iyyarsa, saboda haka ya bukaci kotu ta cireshi daga matsayin gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel