Wawure N16B: Tsohon shugaban 'yansandan Najeriya ya iso gaban alkali

Wawure N16B: Tsohon shugaban 'yansandan Najeriya ya iso gaban alkali

- An fahimci cewa karkashin shugabancinsa, Sunday Ehindero, ya kwashi N64b

- An kama wasu kadarori nasa an kuma kama shaidu an kai kotu

- Ga alama duk wanda yaje babbar kujera a kasar nan kokarinsa ya arzurta kansa da biliyoyi

Wawure N64B: Tsohon shugaban 'yansandan Najeriya ya iso gaban alkali

Wawure N64B: Tsohon shugaban 'yansandan Najeriya ya iso gaban alkali

Mai magana da yawun hukumar yaki da tu'annati ta kasa, Rasheedat Okoduwa, tace a kwanakin nan za'a dawo sauraren karar gwamnati a kotu, inda ake zargin tsohon shugaban 'yansanda Mista Sunday Ehindero, da wawashe kudin 'yansanda, biliyoyi.

An dai kama motoci, gidaje, da manyan kadarori ciki har da shelikwapta makale da sunan tsohon dansandan, wadanda kuma mallakin hukumar ne.

An ga alamun cewa da yawa daga cikin masu inufom na kasar nan suna kokarin arzurta kansu zaras sun yi babbar kujera.

DUBA WANNAN: Duk wanda baya baiwa coci 10% daga dukiyarsa to wuta zai je- Babban Paston Najeriya

Suma dai 'yan siyasar ba'a barsu a baya ba, inda sukan wawure kudaden gwamnati su mayar na kansu, kuma ba karamar sata suke yi ba, biliyoyi suke sacewa.

A shekarar 2012 ne ake sa rai shugaban 'yansandan ya kwashe kudaden na hukumar 'yansanda, kusan biliyan 16, inda ya mayar dasu na cefanensa.

Wasu daga kudaden, gudummanwar jihohi ce domin inganta tsaro a yankinsu, amma aka dinga raba su a bankuna domin badda sawunsu, musamman WEMA bank da Intercontinental.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel