Hukuncin kotu kan Malabu: Adoke bayyi laifin komai ba kan biyayya ga Jonathan

Hukuncin kotu kan Malabu: Adoke bayyi laifin komai ba kan biyayya ga Jonathan

- Tsohon Antoni Janar na kasar nan lokacin Jonathan ya sami wankin kotu

- Har yanzu ana batun Malabu, rijiyar mai da ake ta tababa akai shekaru 10+

- Babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta yanke hukuncin a Abuja

Hukuncin kotu kan Malabu: Adoke bayyi laifin komai ba kan biyayya ga Jonathan

Hukuncin kotu kan Malabu: Adoke bayyi laifin komai ba kan biyayya ga Jonathan

An sami hukunci daga babbar kotun tarayya a yau juma'a daga Abuja, inda kotun ta wanke tsohon Antoni Janar na kasar nan kan batun Malabu da ya lakume kudi har dala biliyan daya da rabi, hukuncin yace ummarni ne kawai Muhammad Bello Adoken yabi.

Jastis Binta Nyako, tace kotu tayi la'akari da koken Mista Adoke, da ma sashen kundiin tsarin mulki da ya baiwa shugaban kasa dama yayi aiki ta hannun miniistocinsa.

Adoken dai tun a bara, ya ce kotu tayi watsi da karar saboda EFCC ta kama shi ne ba bisa ka'ida ba, kuma gwamnati ta kasa tuhumar shuugaba Jonathan ne, ta bige da kama Ministoci kan aikinsu.

DUBA WANNAN: Duk wanda baya baiwa coci 10% daga dukiyarsa to wuta zai je- Babban Paston Najeriya

Antoni Janar na yanzu, Abubakar Malami ne ya shigar da karar, inda yace lallai kotu ta hukunta tsohon antoni Janar din don zamba da badakala.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel