Bamu gane ba, anyi yamma da kare: An kama wani mai adawa da Buhari a yayin zanga zangar yan Shia

Bamu gane ba, anyi yamma da kare: An kama wani mai adawa da Buhari a yayin zanga zangar yan Shia

Jami’an Yansanda dake babban birnin tarayya Abuja sun tarwatsa mabiya addinin Shi’a da barkonon tsohuwa yayin da suke gudanar da zanga zangar kin jinin gwamnati tare da bukatar an sako musu shugabansu, Ibrahim Zakzaky.

Daily Nigerian ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Juma’a 13 ga watan Afrilu, inda baya da tarwatsa yan shi’an, Yansanda sun yi caraf da wani kasurgumin dan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Deji Adeyanju a yayin zanga zangar.

KU KARANTA: An ja kunnen gwamnati game da shigo da amfanin gona da aka sarrafa su da ilimin kimiyya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Deji na daya daga cikin wadanda suke baiwa yan shi’ar goyon baya bisa zaman dirshan da suka kwashe tsawon lokaci suna yi a babban birnin tarayya a Abuja don ganin an sako Zakzaky da gwamati ta kama tun a shekarar 2015.

Bamu gane ba, an yi gabas da kare: An kama wani mai adawa da Buhari a yayin zanga zangar yan Shia

zanga zangar yan Shia

Sai dai majiyar ta kara da cewa wannan kame na Deji ya biyo bayan bukatar yin haka da wata kungiyar magoya bayan Buhari ta yi ne a yan kwanakin da suke wuce, inda suka nemi a kama Deji bisa batanci da yayi ma shugaban kasa a yayin wata hira da aka yi da shi a wata gidan Talabijin.

Bamu gane ba, an yi gabas da kare: An kama wani mai adawa da Buhari a yayin zanga zangar yan Shia

Deji Adeyanju

A cikin wannan hira, Deji yayi ikirarin cewa a isar shugaban kasa Muhammadu Buharo birnin Landanda ke da wuya, wai aka wuce da shi zuwa wata Asibiti don duba lafiyarsa. Sai dai Deji yace “idan basu kama ni ba, ragwage ne su.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel