Karya ta kare: Sojoji sun damke wasu yan bindiga guda 3 a jihar Kaduna (Hotuna)

Karya ta kare: Sojoji sun damke wasu yan bindiga guda 3 a jihar Kaduna (Hotuna)

Jami’an rundunar Sojan kasa sun cika hannu da wani gungun yan bindiga na mutane uku a yayin da suke gudanar da aikin kakkabe yan bindiga a jihar Kaduna, kamar yadda Kaakakin rundunar ya tabbatar.

Sojojin sun samu wannan nasara ne a kauyen Rijana, dake cikin karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna, inda suka kama yan bindiga har sun uku, kamar yadda Kaakaki, Birgediya Texas Chukwu ya bayyana.

KU KARANTA: Hare haren Yan bindiga: Sanata Shehu Sani ya zargi El-Rufai da daukan nauyin yan bindiga a Jihar

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin yana cewa tuni sun fara gudanar da binciken kwakwaf akan yan bindigan don tabbatar da irin rawar da suka taka a baya wajen tayar da hankulan jama’an yankin.

Karya ta kare: Sojoji sun damke wasu yan bindiga guda 3 a jihar Kaduna (Hotuna)

Yan bindigan

Daga karshe sanarwar ta bukaci jama’a dasu cigaba da basu goyon bayan, tare da taimaka ma Sojoji da sauran hukumomin tsaro da bayanan sirri masu muhimmanci.

A wani labarin kuma, wasu yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar birnin gwari na jihar Kaduna, inda suka kashe Yansanda guda biyu tare da yin awon gaba da mutane goma sha takwas.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel