Atiku ya sake kira ga yiwa Najeriya gyara

Atiku ya sake kira ga yiwa Najeriya gyara

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga sake gyaran tarayyar Najeriya da kuma karawa kananan sassan gwamnati karfi

- Ya bukaci shuwagabannin kasa da subi hanyoyin da suka dace don taimakawa wurin magance matsalolin dake damun kasar

- Yace kasar yanzu tana da abubuwa wadanda tasa a gabanta kamarsu makarantu, hanyoyi, da asibitoci banda hannayen jari da gwamnatin tasa a gaba tana bayarwa

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga sake gyaran tarayyar Najeriya da kuma karawa kananan sassan gwamnati karfi.

Ya bukaci shuwagabannin kasa da subi hanyoyin da suka dace don taimakawa wurin magance matsalolin dake damun kasar musamman na tsahe tashen hankula. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a birnin tarayya.

Atiku ya sake kira ga yiwa Najeriya gyara

Atiku ya sake kira ga yiwa Najeriya gyara

Yace kasar yanzu tana da abubuwa wadanda tasa a gabanta kamarsu makarantu, hanyoyi, da asibitoci banda hannayen jari da gwamnatin tasa a gaba tana bayarwa. Inda yace baza’a samu nasarar yin hakaba sai ta hanyar yin yarjejeniya da kowane bangare na kasar.

KU KARANTA KUMA: Mai bada shaida akan shari’an Babangida Aliyu ya fadi summame ana cikin shari’a

Yace bai kamata ace duka helikwata hadda ta kananan hukumomi anyisu a birnin tarayya ba, saboda yana nuna cewa duk wata matsala hada jiha dole sai anje helikwata sannan a magance ta wanda kuma hakan ke kara kawo rashawa a cikin al’amurra.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel