Kudin satar Abacha: Majalisar wakilai ta shirya bincikar ministan Buhari

Kudin satar Abacha: Majalisar wakilai ta shirya bincikar ministan Buhari

Majalisar wakillan Najeriya a jiya sun yanke shawarar bincikar ministan Shari'a na tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa wasu kudin da aka ce an kwato na satar da marigayi tsohon shugaban kasa Sani Abacha.

A duka cikin harkallar dai, ana zargin Ministan Shari'ar da ware wasu makudan kudaden da suka kai Dalar Amurka 16.9 inda ya biya wasu manyan lauyoyin kasar nan na aikin da suka yi.

Kudin satar Abacha: Majalisar wakilai ta shirya bincikar ministan Buhari

Kudin satar Abacha: Majalisar wakilai ta shirya bincikar ministan Buhari

KU KARANTA: Yan shi'a ku cigaba da zanga-zangar ku - Falana

Legit.ng ta samu kuma cewa 'yan majalisar ta wakillai sun bukaci gwamnatin tarayyar da ta gaggauta tsayar da biyan kudaden nan har sai ta kammala binciken ta game da su.

A wani labarin kuma, Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Mista Prince Uche Secondus a jiya ya kwarmatawa tawagar tarayyar kasashen Turai da suka kai masa ziyara a ofishin sa cewa tuni jam'iyya mai mulki ta APC ta kammala hada baki da hukumar zabe ta INEC domin yin murdiya a zaben 2019 mai zuwa.

Mista Secondus dai ya yi wannan ikirarin ne lokacin da tawagar kungiyar kasashen ta tarayyar Turai karkashin jagorancin Ketil Karlsen suka kai masa ziyarar ban girma a babbar Sakatariyar jam'iyyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel