Mai bada shaida akan shari’an Babangida Aliyu ya fadi summame ana cikin shari’a

Mai bada shaida akan shari’an Babangida Aliyu ya fadi summame ana cikin shari’a

- Tsohon Daraktan ma’aikatar filaye Mohammed Shaba Yabagi, ya suma lokacin da aka fara sauron karagame da tsohon gwamna Mu’azu Babangida Aliyu da hukumar EFCC na zarginsa da hukumar keyi da aikata damfara

- Tsohon gwamnan da Umar Muhammad Nasko tsohon kwamishinan filaye, wuraren hutawa, wuraren shakatawa da kuma dazuzzuka sune ake zargi da lafifuka takwas, na dibar kudade kimanin N2bn

- Yabagi wanda yana daya daga cikin shaidun wadanda ake kara ya fadi ya suma a cikin kotu lokacin da wakilin EFCC Prince Ben Ikani ke bincikar sa a kotun

Tsohon Daraktan ma’aikatar filaye Mohammed Shaba Yabagi, ya suma lokacin da aka fara sauron karagame da tsohon gwamna Mu’azu Babangida Aliyu da hukumar EFCC na zarginsa da hukumar keyi da aikata damfara.

Tsohon gwamnan da Umar Muhammad Nasko tsohon kwamishinan filaye, wuraren hutawa, wuraren shakatawa da kuma dazuzzuka sune ake zargi da lafifuka takwas, na dibar kudade kimanin N2bn.

Mai bada shaida akan shari’an Babangida Aliyu ya fadi ya suma ana cikin shari’a

Mai bada shaida akan shari’an Babangida Aliyu ya fadi ya suma ana cikin shari’a

A lokacin da aka fara shari’ar a kotun tarayya a garin Minna, a ranar Laraba, Yabagi wanda yana daya daga cikin shaidun wadanda ake kara ya fadi ya suma a cikin kotu lokacin da wakilin EFCC Prince Ben Ikani ke bincikar sa a kotun.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan Shi’a ku cigaba da zanga-zangar ku - Falana

Hakan ya janyo dole kotu ta bayar da hutu na dan lokaci kafin mai bayar da shaidan ya farfado, don bayar da shaida. Wani tsohon Perm. Sec. na ma’aikatar ayyuka Malam Umaru Bawa, ya bayyana yadda aka samu kudaden daga gwamnatin tarayya don bayar da kwangilolin ayyuka, duk da dai yace ba a aiwatar da wasu cikin kwangilolin ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel