Tazaren Buhari: Dinbin 'Yan siyasa na shirin tserewa daga Jam’iyyar APC

Tazaren Buhari: Dinbin 'Yan siyasa na shirin tserewa daga Jam’iyyar APC

- Wasu da dama za su bar APC bayan Shugaba Buhari yace zai zarce

- ‘Yan siyasan Arewa dai sun san ba za su kai labari ba a zabe na 2019

- Ana zargin cewa masu harin kujerar Buhari za su nemi su koma PDP

Mun ji cewa akwai alamun cewa wasu manyan ‘Yan Jam’iyya na shirin tserewa daga APC mai mulki a dalilin jin labarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai sake takara a zabe mai zuwa. Watakila dai wasu a APC za su bi Atiku Abubakar zuwa PDP.

Tazaren Buhari: Dinbin 'Yan siyasa na shirin tserewa daga Jam’iyyar APC

Wasu 'Yan siyasa daga Arewa na shirin barin Jam’iyyar APC

Jaridun kasar nan sun rahoto cewa wasu daga cikin ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC za su tattara su bar Jam’iyyar kafin zaben 2019 bayan da Shugaban kasa Buhari ya tabbatar da cewa da shi za a nemi takara a zabe na gaba kuma a karkashin Jam’iyyar.

KU KARANTA: PDP ta firgita Shugaba Buhari inji Sule Lamido

Wata Majiya ta bayyana mana cewa tsofaffin Gwamnonin kasar da masu shirin barin gado da wasu manyan ‘Yan Majalisan kasar musamman wadanda su ka fito daga Yankin Arewa sun san babu labari a zabe mai zuwa idan har Shugaba Buhari yana APC.

Akwai dai wasu ‘Yan siyasa a Arewa da ke harin kujerar Shugaban kasar kuma zai yi wahala su iya kai labari ganin cewa Shugaba Buhari zai nemi ya zarce a 2019. Zai ma dai yi wuya wani ya iya tsayawa takaran fitar da gwani na Jam’iyyar APC da Buhari

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel