Fashewar Bam ta kashe mutane 5 yayin wasan kwallon kafa a kasar Somalia

Fashewar Bam ta kashe mutane 5 yayin wasan kwallon kafa a kasar Somalia

Da sanadin shafin kamfanin dillancin labarai na Najeriya, a ranar Juma'ar da ta gabata ne muka samu rahoton cewa wani harin bam ya kashe mutane biyar yayin gudanar da wasan kwallon kafa a kudancin kasar Somalia.

Bam din dai ya fashe ne a farfajiyar wasanni ta garin Barawa dake karkashin yankin Shabelle yayin da al'umma da dama ke kallon wasan na kwallon kafa da tsakar ranar Alhamis din da ta gabata.

Jami'an hukumar 'yan sanda na kasar sun hasashen kungiyar Al Qaeda gami da Al Shabaab ke da alhakin wannan ta'addanci da ya afku.

Fashewar Bam ta kashe mutane 5 yayin wasan kwallon kafa a kasar Somalia

Fashewar Bam ta kashe mutane 5 yayin wasan kwallon kafa a kasar Somalia

Hukumar ta kuma bayyana cewa, anyi amfani da fasahar zamani wajen tayar da bam din daga nesa ba tare da kusantar sa ba, inda rayukan mutane biyar suka salwanta tare da raunatar wasu dama a filin na kwallo.

KARANTA KUMA: Kotu ta fitar da ranar ci gaba da zama kan batun Patience Jonathan

Mahad Dhoore, Wani dan majalisa na yankin Kudu maso Yammacin kasar da harin ya afku a kan idan sa yayin da yake kallon wasan kwallon kafa ya yi Allah wadai da wannan abin takaici.

Muhammad Aden, wani jami'in dan sanda ya bayyana cewa kungiyar Al Shabaab ake zargi da wannan aika-aika da ta afku

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kungiyar Al Shabaab ita kadai ce makiya ga kasar Somalia kamar yadda shugaban ta Muhammad Abdullahi Muhammad ya bayyana a yayin wata liyafar bankwana da aka shiryawa kakakin majalisa na kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel