Taron PDP ne ya firgita Buhari ya ce zai yi takara - Sule Lamido

Taron PDP ne ya firgita Buhari ya ce zai yi takara - Sule Lamido

Rahotanni sun kawo cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido yayi ba’a ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC.

Yace jam’iyyar shugaban kasar ta tsorata ne da taron da PDP ta gudanar a jihohin Jigawa da Katsina shiyasa suka roke shi ya bayyana kudirinsa na sake takara.

Lamido ya ce: ''Ai taron da aka yi a Jigawa da na Katsina shi ya firgita su, suka ce ranka ya dade gara fa ka zo, domin yadda aka yi taron nan na Jigawa da Katsina, idan ba ka zo ka ce za ka yi takara ba mun shiga uku.''

A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyyarsa ta kara tsayawa takara a zaben 2019.

Taron PDP ne ya firgita Buhari ya ce zai yi takara - Sule Lamido

Taron PDP ne ya firgita Buhari ya ce zai yi takara - Sule Lamido

Tsohon gwamnan ya kara da cewa APC da Buharin sun yi hakan ne domin su samu dan hutu na ''Tsunamin'' da PDP ta yi a jihohin biyu a tarukanta.

KU KARANTA KUMA: Kwamitin majalissa 20 ne suke kawo tangarda a sanya hannu ga kasafin 2018 - Saraki

Ya ce sai ma jam'iyyar tasu ta yi irin taron a Sokoto da Kaduna da Kebbi kafin kuma ta yi na Abuja lokacin da hankalin shugaban da jam'iyyarsa za su fi tashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel