Kwamitin majalissa 20 ne suke kawo tangarda a sanya hannu ga kasafin 2018 - Saraki

Kwamitin majalissa 20 ne suke kawo tangarda a sanya hannu ga kasafin 2018 - Saraki

- Shugaban majalissa Bukola Saraki ya bayyana kwamitoci 20 na majalissa wadanda ke kawo tangarda game da sanya hannu ga kasafin kudi na 2018

- Saraki ya gargadi kwamitocin da kadasu kawowa Najriya tangarda sakamakon kin gabatar da rahoton kasafin kudinsu

- Yace ya zama dole ya bayyana sunayen kwamitocin don daukar matakin da ya kamata game dasu don cigaban kasar

Shugaban majalissa Bukola Saraki, a jiya ne ya bayyana kwamitoci 20 na majalissa wadanda ke kawo tangarda game da sanya hannu ga kasafin kudi na 2018.

Sarakin cikin damuwa, ya gargadi kwamitocin da kada su kawowa Najriya tangarda sakamakon kin gabatar da rahoton kasafin kudinsu ga majalissar.

Kwamitin majalissa 20 ne suke kawo tangarda a sanya hannu ga kasafin 2018 - Saraki

Kwamitin majalissa 20 ne suke kawo tangarda a sanya hannu ga kasafin 2018 - Saraki

Saraki yace ya zama dole ya bayyana sunayen kwamitocin don daukar matakin da ya kamata game dasu don cigaban kasar.

Yace an bawa wadannan “kwamitoci 20 wa’adi na gabatar da rahotanninsu a yau juma’a”.

Majalissun biyu sun yanke cewa zasu kaddamar da kasafin na 2018 a ranar 24 ga watan Afirilu, saboda watanni bakwai kenan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da musu da kasafin bayan ya sanya hannu, a ranar 7 ga watan Nuwamba na 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel