Najeriya ta fara hangen yadda za ta amfana da $770m na tallafin UN

Najeriya ta fara hangen yadda za ta amfana da $770m na tallafin UN

Kasar Najeriya ta fara hangen yadda za ta amfana da tallafin Dalar Amurka miliyan 770 wajen alkintawa tare da inganta mu'amalan hukumar kula da manyan hanyoyi domin rage afkuwa hadurra da kaso 50 cikin 100 zuwa shekarar 2030.

Jakadan kasar Najeriya a majalisar dinkin duniya, Mista Akinremi Bolaji, shine ya bayyana hakan yayin gabatar da jawaban kasar sa a babban ofishin majalisar dake birnin New York na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Bolaji ya yi wannan jawabi ne a yayin kaddamar da shirin majalisar dinkin duniya na bayar da tallafin inganta manyan hanyoyi.

Bolaji yake cewa, a matsayin Najeriya kasa mai tasowa ta fuskar ci gaba, baya ga goyon bayan wannan shiri da take yi ta kuma fara zuba idanu domin ta kasance cikin sahun farko na kasashen da za su amfana da wannan tallafi.

KARANTA KUMA: An tsinci gawar kananan yara 2 cikin Firinji a jihar Ondo

Ya ci gaba da cewa, muddin Najeriya ta samu wannan tallafi to kuwa afkuwar hadurra za su ragu da kimanin kaso 50 cikin 100 wanda daman ita ce babbar manufa ta majalisar dinkin duniya.

Jakadan na Najeriya ya kuma yabawa majalisar dinkin duniya dangane da wannan shiri da ta sanya a gaba na cimma manufa ta ingantawa tare da bayar da kulawar tsaro da kariya ga manyan hanyoyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel