Yan bindiga sun kashe yan sanda sannan suka sace amare 2 a Kaduna

Yan bindiga sun kashe yan sanda sannan suka sace amare 2 a Kaduna

An harbe wasu jami’an yan sanda biyu da kuma wani jami’in kungiyar NURTW har lahira a kauyen Ciki Da Falo dake karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa da majiyarmu a ranar Alhamis, inda yace an sace mutane 15 ciki harda amare biyu.

Mazaunin yankin wanda yayi Magana bisa sharadin sirrinta sunasa yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 5pm na ranar Alhamis.

Austin Iwar, kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, ya tabbatar da lamarin amma bai bada cikakken bayani ba.

An tattaro cewa an kashe jami’an ne a bakin aiki a garin.

KU KARANTA KUMA: Duk wani dan takarar shugaban kasa da PDP zata tsayar sai ya kayar da Buhari - Secondus

Kamar yadda dai kuka sani Birnin Gwari ya kasance matattara na yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane domin kudin fansa.

A makonni biyu da suka shige, Zubairu Gwari, sarkin Birnin Gwari ya bukaci jama’arsa da su kare kansu daga masu kai hare-hare garuruwansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel