Dole Najeriya ta sanya karin kudi a harkar kiwon lafiya - WHO

Dole Najeriya ta sanya karin kudi a harkar kiwon lafiya - WHO

- Najeriya ta kara hannun jari a fannin lafiya - inji shugaban majalisar kiwon lafiya ta duniya.

- Shugaban majalisar kiwon lafiya ta duniya, Tedros Ghebreyesus ya shawarci Najeriya ta kara hannun jari a fannin kiwon lafiya

Dole Najeriya ta sanya karin kudi a harkar kiwon lafiya - WHO

Dole Najeriya ta sanya karin kudi a harkar kiwon lafiya - WHO

Mista Ghebreyesus ya bada wannan shawarar ne a taron na biyu na THISDAY a ranar Alhamis a Abuja. Taron dai wanda jaridar THISDAY ta dau nauyi da taimakon, ma'aikatar lafiya ta tarayya, Bankin duniya, majalisar kiwon lafiya ta duniya, UNICEF, UNFPA da kuma USAID.

Mista Ghebreyesus yace sabon tsarin majalisar na shekaru biyar shi ne ganin cewa sama da mutane biliyan daya su samu damar amfana da Universal Health Coverage (UHC) nan da 2023.

Kamar yadda yace fiye da rabin mutanen duniya basu da damar samun ingantatacciyar kiwon lafiya. Kuma kusan mutum miliyan 100 ne suke fadawa tsananin talauci duk shekara sakamakon kudaden kiwon lafiya da suke biya.

Tace UHC yafi shirin inshorar lafiya. Yana nufin samarda ingantattun kiwon lafiya, a duk inda suke kuma a duk lokacin da bukatar hakan ta taso ba tare da wani matsi ko takura ba.

Yace ginshikin kiwon lafiya mai dorewa ya dogara ne da yanda kasar ta ke daukan matakan karewa da kuma daukaka guraren kiwon lafiya. Wadannan wuraren kiwon lafiya su na zama kariya ne gurin barkewar annoba. Samarda UHC zai Bude wata dama ne na maida kudurorin siyasa zuwa riba, sannan da farfado da cibiyoyin kiwon lafiya.

Ministan ma'aikatar lafiya, Isaac Adewole yace za a dinga Kiran shirin "Huwe" ma'anar shi "Rayuwa" a harshen Ebira. Mista Adewole yace Huwe cikon aikin da Gwamnatin jiha da ta kananan hukumomi sukeyi ne don inganta bangaren lafiya.

DUBA WANNAN: 'Abin da Buhari yayi a shekara uku yafi na Obasanjo a shekaru takwas'

Ministan ya kara da cewa shirin zai samarda kudi domin ceto rayuka da kuma taimakon gaggawa ga duk yan'najeriya

Uwargidan shugaban majalisar dattijai Toyin Saraki tace UHC ba wai zata samarda cibiyoyin kiwon lafiya bane kadai, har da rage fatara, samar da aikin yi, cigaban tattalin arziki da sauransu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel