'Abin da Buhari ya cimma a shekaru uku sun fi wadanda Obasanjo yayi a shekaru takwas

'Abin da Buhari ya cimma a shekaru uku sun fi wadanda Obasanjo yayi a shekaru takwas

- Obasanjo baya so shugaba Buhari ya fishi shanawa

- Obasanjo na neman taron dangi a kayar da Buhari a 2019

- Shekaru uku da Buhari yayi akan mulki, yafi shekaru takwas da Obasanjo yayi- inji Tony Momoh

'Abin da Buhari ya cimma a shekaru uku sun fi wadanda Obasanjo yayi a shekaru takwas

'Abin da Buhari ya cimma a shekaru uku sun fi wadanda Obasanjo yayi a shekaru takwas

Tsohon ministan yada labarai wanda kuma shine shugaban tsohuwar jam'iyyar Congress for Progressives Change wacce daga baya sukayi maja da wasu jam'iyyun suka samar da All Progressives Congress (APC), Prince Tony Momoh yayi magana akan bayyanawa da shugaba muhammadu Buhari yayi na son sake fitowa takarar shugabancin kasar,wasikar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kuma cigaban da ake samu a jam'iyya mai ci yanzu a wata zantawa da sukayi da Temidayo Akinsuyi a Abuja.

"Ina siyasa ne saboda Buhari. Idan yau Buhari yace ya bar siyasa toh nima zan barta domin ba abinda siyasa zata bani. Al'ummata ta bada ni don inyi aiki tare da Buhari a 2003.

Abinda mutanenmu basu gane ba shine, bai kamata mu dubi abinda Buhari bai yi ba, kamata yayi mu dubi abinda zai iya faruwa in ba shi ke mulkin ba. Abuja da muke zaune da tuni Boko Haram sun wargaza ta. Wani abin jinjiinawa ga shugaban shi ne yanda muka dena shigo da abinci da kuma yanda tattalin arzikinmu ya farfado.

DUBA WANNAN: Ku biya Yesu kudi ko ya sanya ku a wuta

Obasanjo ya fito daga gidan yari da matsananciyar fatara, a shekaru uku na farkon mulkin shi yayi su ne don samo kanshi, shekarun karshen kuwa yayi su ne gurin tara dukiya. A sakamakon haka ne wadannan shekaru 8 din suka zama mana mafi muni a tarihin damokaradiyyar kasar nan.

A cikin kwanakin nan ne PDP suka ba ma yan'najeriya hakuri akan barnar da sukayi na tsawon shekaru 16,a tunaninsu bada hakuri kadai ya wadatar da har zamu kara basu wata dama?

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel