An damke wani dan shekaru 22 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade

An damke wani dan shekaru 22 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade

- An cafke wani matashi da yayi wa yarinya yar shekara 12 fyade a jihar Neja

- Matashin yayi alkawarin siyawa yarinyar kyauta ne amma da suka hadu sai ya kaita wani kebaban wuri yayi lalata da ita

- Matashin ya amsa cewa yasan yarinya ce karama amma wai yana son ya aure ta ne idan ta kara girma

Hukumar Yan sanda reshen jihar Neja sun bayar da sanarwar kama wani matashi mai shekaru 22 mai suna Chukwuebuka Nnaji bisa laifin yiwa wata karamar yarinya mai shekaru 13 fyade.

Lamarin ya faru ne a unguwar Madalla dake karamar hukumar Suleja na Neja. An gano cewa Nnaji ya ce yarinyar ta same shi a wani Otal dake unguwar Madalla inda yace akwai kyautar da zai bata.

An damke wani dan shekaru 22 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade

An damke wani dan shekaru 22 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade

DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya ta gudanar da bikin nuna kwalliyar mata a karo na farko

Rahotanni sun bayyana cewa da isar yarinyar harabar Otal din, Nnaji ya tasa kayarta zuwa wani kebaban wuri a daji kuma yayi lalata da ita.

Wanda ake tuhumar wanda yana zaman a shago ne ya ce, "Na san cewa ita karamar yarinya ne hakan yasa banyi mata ciki ba. Ina son sai ta kara girma kafin in aure ta."

Ya cigaba da cewa, "Na sadu da ita ne saboda ina son in kawar mata da budurcinta amma daga baya sai na gane cewa sha'awa ce kawai ta mamaye ni."

Kakakin hukumar Yan sanda na jihar, Muhammad Abubakar yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa lokacin da ake masa tambayoyi kuma nan da bada dadewa ba za'a gurfanar dashi gaban kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel