Duk wani dan takarar shugaban kasa da PDP zata tsayar sai ya kayar da Buhari - Secondus

Duk wani dan takarar shugaban kasa da PDP zata tsayar sai ya kayar da Buhari - Secondus

A ranar Alhamis, 12 ga watan Afrilu, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tace ta shirya tunkarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da yaki a zaben shugaban kasa wanda za’a yi a 2019.

Da yake hira da jaridar Daily Independent a Abuja, Prince Uche Secondus, shugaban jam’iyyar na kasa yace duk wani dan takara da jam’iyyar zata tsayar a matsayin dan takarar shugaban kasa zai kayar dad an takarar APC, harma da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da cewa zai sake takara a taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar.

Duk wani dan takarar shugaban kasa da PDP zata tsayar sai ya kayar da Buhari - Secondus

Duk wani dan takarar shugaban kasa da PDP zata tsayar sai ya kayar da Buhari - Secondus

A cewar Secondus, babu yadda zaa yi yan Najeriya sun zabe su bayan wahalar da suka fuskanta a karkashin wannan gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Muna biyan N1.5b ga talakawan Najeriya duk wata - Osinbajo Muna biyan N1.5b ga talakawan Najeriya duk wata - Osinbajo

Sannan kuma cewa gwamnatin ta gaza cika dukka alkawaran da ta daukarwa al’umma a zaben 2015.

Ya lissafa cewa ga koma bayan tattalin arziki, rashin ayyukan yi, tsadar rayuwa, rashin tsaro, rasa aiki a kullun, da kuma bangaranci a wajen yaki da rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel