Idan ba mu inganta tsaro mun samawa matasa aiki ba kar ku zabe mu Inji Saraki a 2014

Idan ba mu inganta tsaro mun samawa matasa aiki ba kar ku zabe mu Inji Saraki a 2014

- Bukola Saraki yayi alkawarin cewa Gwamnatin APC za ta gyara Najeriya

- Saraki yace idan har su ka gaza samawa Najeriya to ka da a sake zaben su

- Shekaru 4 da yin wannan maganar ga shi mun dawo da ita domin a auna

Wannan karo mun kawo wasu alkawuran da Bukola Saraki ya dauka a madadin Jam’iyyar APC a lokacin su na yakin neman zaben 2015. Wadannan alkawura dai su ne Shugaban kasa Buhari ya dauka da bakin sa shekaru 4 da su ka wuce.

Idan ba mu inganta tsaro mun samawa matasa aiki ba kar ku zabe mu Inji Saraki a 2014

Bukola Saraki yayi alkawarin cewa APC za ta gyara Najeriya

Ga dai jerin alkawuran nan mun kawo su:

1. Rashin aikin yi

Bukola Saraki wanda ya zama Shugaban Majalisar Dattawa yace idan Gwamnatin APC ta gaza samawa jama’a aikin yi, to ka da a zabe ta a 2019. Yanzu dai an samu karuwar rashin aikin yi a Najeriya a Gwamnatin na APC.

KU KARANTA:

2. Inganta tsaro

A lokacin yakin neman zabe, Bukola Saraki ya bayyana cewa za su inganta tsaro a Najeriya. Ko da dai an samu galaba sosai a kan Boko Haram, ana kuma fama da barazanar Makiyaya da masu garkuwa da mutane da sauran barna a kasar.

3. Saukin rayuwa

A ranar 14 ga Watan Yuli ne Bukola Saraki ya rubuta a shafin sa na Tuwiya cewa za su samawa ‘Yan Najeriya saukin rayuwa. Sai dai kuma a wannan Gwamnati ne kaya su kayi tsada wanda ya sa jama’a su ka tagayyara kwarai da gaske.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel