Muna biyan N1.5b ga talakawan Najeriya duk wata - Osinbajo

Muna biyan N1.5b ga talakawan Najeriya duk wata - Osinbajo

Mataimakin shugabna kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati mai ci na biyan naira 5,000 du wata ga talawa sama da 300,000 a fadin kasar.

Mataimakin shugaban kasar yace ana wannan biyan ne ba tare da duba ga jam’iyyar da mutun yake ba.

Da yake Magana a ranar Alhamis a Umuahia wajen kaddamar da Abia State Tele-Health Support Centre, Osinbajo yace gwamnatin taeayya ta bayar da bashi gay an kasuwa sama da 300,000, ciyar da dalibai 125,624 a makarantu 742 “sannan kuma muna da masu girka abinci 1,569 da aka ba bashi karkashin shirin GEEP, mun kuma bayar da bashi ga masu kananan sana’o’i 7,585.”

Muna biyan N1.5b ga talakawan Najeriya duk wata - Osinbajo

Muna biyan N1.5b ga talakawan Najeriya duk wata - Osinbajo

Ya ce zuwa yanzu gwamnati ta zuba kimanin naira biliyan 2.4 a jihar Abia musamman a fannin lafiya, muna da shirin ceto rayuka miliyan daya, wanda muka bayar dad ala miliyan 1.5 ga ko wacce jiha ciki harda jihar Abia, domin inganta asibitocin gwamnati dake nan musamman saboda matanmu da yara.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga: ‘Yan Shi’a sun hana kowa sakat a Birnin Tarayya Abuja

Maataimakin shugaban kassar yace shirin gwamnatin tarayya ga kasar ya kasance ga lafiyar dukkanin yan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel