Zanga-zanga: ‘Yan Shi’a sun hana kowa sakat a Birnin Tarayya Abuja

Zanga-zanga: ‘Yan Shi’a sun hana kowa sakat a Birnin Tarayya Abuja

- Magoya bayan Shi’a sun yi wata zanga-zangar lumana a cikin Abuja

- Daruruwan ‘Yan Shi’a sun hau kan titi sun cika Birnin Tarayya a jiya

- ‘Yan Shi’an sun nemi a saki babban Malamin su da yake tsare har yau

Mun samu labari daga Jaridar Sahara Reporters cewa ‘Yan kungiyar IMN na Shi’a sun yi gagarumar zanga-zanga a babban Birnin Tarayya Abuja a jiya Alhamis inda su ka cika Garin su ka hana masu zirga-zirga sukuni.

Zanga-zanga: ‘Yan Shi’a sun hana kowa sakat a Birnin Tarayya Abuja

‘Yan Shi’a sun yi kira a saki Ibrahim El-Zakzaky

Kamar yadda mu ka samu labari Mabiya Shi’an sun yi wata zanga-zangar lumana ne a cikin Birnin Tarayya Abuja domin tunawa da Jama’an su da su ka rasa rayukan su wajen gwagwarmaya a Duniya inji Sheikh AbdulHamid Bello.

KU KARANTA: An yankewa wani Alkali zaman kaso na shekaru 3

Kamar yadda Jagoran na Shi’a a wajen taron ya bayyana, a wata irin na Rajab, su kan ware ranaku domin su tuna da Shahidan su a fadin Duniya. Daga ciki akwai harin aka kai masu a karshen Disamban 2015 inda aka rasa manya da yara.

A karon da su kayi da Sojoji ne dai aka yi gaba da Jagoran Kungiyar IMN a Najeriya watau Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda har yanzu ya ke tsare a hannun Hukuma. ‘Yan Shi’ar su na cigaba da zanga-zanga na ganin cewa an saki babban Malamin na su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel