An nemi ‘Dan Majalisar da ya zagi Shugaban kasa Buhari ya ba mutanen Najeriya hakuri

An nemi ‘Dan Majalisar da ya zagi Shugaban kasa Buhari ya ba mutanen Najeriya hakuri

- Wani Sanatan PDP ya soki Shugaban kasa Buhari a zaman Majalisa

- Sanata Abaribe ya jawo rikici a Majalisar da ya zagi Shugaban kasar

- Wata Kungiya tace akwai bukatar Sanatan ya nemi gafarar ‘Yan kasa

Mun samu labari cewa Sanatan Jihar Abia Eyinayya Abaribe ya gamu da suka da Allah-wadai daga Kungiyar BMSG na Magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon nan wanda tace ya kamata ya nemi afuwar ‘Yan kasa.

An nemi ‘Dan Majalisar da ya zagi Shugaban kasa Buhari ya ba mutanen Najeriya hakuri

Abaribe ya jefa Majalisa cikin hatsaniya da ya soki Buhari

Idan ba ku manta ba, Sanatan na Jam’iyyar adawa ya fadi kalamai marasa dadi game da Shugaban kasar. Kungiyar ‘Yan ga-ni-kashe-nin Buharin tace Sanatan ya jawowa Majalisar Dattawan kasar abin kunya ne da wadannan kalaman na sa.

KU KARANTA: 'Yan Sanda na neman Shehu Sani a Garin Kaduna

Ba Sanatan na Abia kadai ba, Magoya bayan Shugaba Buhari sun yi kaca-kaca da ‘Yan Majalisan da ke labewa karkashin martabar kujerar su wajen zagin Shugaban kasar. Sanata Abaribe dai yace ne Shugaba Buhari bai san abin da yake yi ba.

Austin Braimohn da Cassifu Madueke wanda su ne Shugabannin Kungiyar ta BMSG a wani jawabi da su ka fitar jiya Alhamis sun bayyana cewa Sanatan ya nuna cewa babu tsafta a cikin siyasar sa inda su kayi kira ga Majalisa ta ja masa kunne maza.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel