Hare haren Yan bindiga: Sanata Shehu Sani ya zargi El-Rufai da daukan nauyin yan bindiga a Jihar

Hare haren Yan bindiga: Sanata Shehu Sani ya zargi El-Rufai da daukan nauyin yan bindiga a Jihar

Wakilin al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar babu zaman lafiya a Kaduna, inda yan bindiga da mahara makiyaya ke cin karensu babu babbaka a jihar.

Sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na Tuwita, inda yace a Kaduna ta fada halin matsalar tsaro kamar yadda jihohin Benuwe, Zamfara, Taraba da Neja ke fuskanta, inda ake satar mutane tare da yi musu kisa kiyashi, cikin har da Sojoji.

KU KARANTA: Jarabawar gwaji: Cikin Malaman makarantun sakandari a jihar Kaduna ya duri ruwa

Legit.ng ta ruwaito Sanatan ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da kokarin makure yan jaridu da nufin su daina ruwaito hare haren da yan bindiga ke kaiwa a jihar, wai don kada su kunyata jihar tare da gwamnatin tarayya.

Sani ya kara da cewa a kullum talakawan jihar Kaduna na binne yan uwansu, yayin da gwamnatin jihar ke biyan yan bindigar makudan kudade da sunan kudin fansa domin su daina kai hare haren, inda ya bayyana hakan a matsayin tushen abinda ke kara ma yan bindigan kwarin gwiwa.

Daga karshe yace duk gwamnan dake gwamnandake biyan yan bindiga kudi da nufin su dai kai hare hare, toh shi ne maigidan yan bindigar, shi ne ke daukan nauyinsu, kuma kamata yayi a kama shi, don kuwa ya zama barazanar tsaro a kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel