Uwargidar Shugaba Buhari ta koro Mamman Daura daga Aso Villa

Uwargidar Shugaba Buhari ta koro Mamman Daura daga Aso Villa

- Matar Shugaban kasa tayi waje da Mamman Daura daga cikin Aso Villa

- Akwai rade-radin cewa Daura na zaune ne cikin Fadar Shugaban kasar

- Alhaji Mamman Daura ‘Danuwa ne kuma Aminin Shugaban kasa Buhari

Mun samu labari cewa a kwanan nan ne Uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta kori babban na-gaban-goshin Mai gidan ta Alhaji Mamman Daura daga cikin Fadar Shugaban kasa.

Uwargidar Shugaba Buhari ta koro Mamman Daura daga Aso Villa

Matar Buhari tayi waje da Mamman Daura daga Aso Villa

Kamar yadda labari yake zuwa mana daga Jaridar Rariya, bisa dukkan alumu Hajiya Aisha Buhari ta rufe gidan da babban Aminin Shugaban kasar watau Alhaji Mamman Daura yake zama ne bayan Shugaba Buhari yayi tafiya.

KU KARANTA: An bar Shugaba Buhari hannu-rabbana a Majalisar Dattawa

IG Wala wani fitaccen ‘dan gwargwamaya a kasar shi ya bayyana cewa Aisha Buhari tayi waje da Mamman Daura daga fadar Aso Villa inda har ta samu wani katon kwado ta rufe gidan da yake zama a cikin fadar Shugaban kasar.

A makon nan ne Shugaban Kasa Buhari ya tattara ya fi Landan inda zai halarci wani taro da Firayim Ministan kasar. Dama dai Matar Shugaban kasar ta dade tana kokawa da cewa akwai wasu da ba kowa ba da su ka zagaye Buhari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel