Karshen tika-tika-tik: Sanatan Kaduna zai yi takara da El-Rufai a 2019

Karshen tika-tika-tik: Sanatan Kaduna zai yi takara da El-Rufai a 2019

- Shehu Sani ya bayyana cewa zai yi takarar Gwamnan Jihar Kaduna

- Sanatan yace mulkin zalunci Gwamna mai-ci Nasir El-Rufai yake yi

- ‘Dan Majalisar yace Gwamnan ya fara shirin barin gidan Gwamnati

Mun samu labari cewa a jiya Alhamis ne Fitaccen Sanatan nan na Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar Gwamnan Jihar Kaduna a zabe mai zuwa idan Allah ya so.

Karshen tika-tika-tik: Sanatan Kaduna zai yi takara da El-Rufai a 2019

Sanatan APC zai yi takara da Gwamna Nasir El-Rufai

Shehu Sani yayi amfani da shafin sa na Facebook inda ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Kaduna na-yanzu watau Nasir El-Rufai yana kokarin amfani da Jami’an ‘Yan Sanda domin bata masa suna da kuma ci masa mutunci.

KU KARANTA: Sanata Shehi Sani ya maidawa El-Rufai martani mai zafi

Sanatan ya nuna cewa yunkurin Gwamnan Jihar ba zai kai ko ina ba. ‘Dan Majalisar yayi wannan jawabi ne da Hausa a shafin sada zumuntar na sa. Shehu Sani ya kara jadadda cewa mulkin kama-karya Gwamnan yake yi.

‘Dan Majalisar dai yace maganar takarar Gwamna kuma kamar yayi ne idan Allah ya so domin ya karbowa Talakawa ‘yancin su daga zaluncin Gwamna Nasir El-Rufai don haka ya fada masa ya fara tattara kayan sa ya bar ofis.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel