Bukola Saraki ya tarwatsa Sanatocin da ke tare da Shugaban kasa Buhari

Bukola Saraki ya tarwatsa Sanatocin da ke tare da Shugaban kasa Buhari

- Bukola Saraki ya watsa magoya bayan Shugaba Buhari a Majalisar Dattawa

- Wasu da ke tare da Shugaban kasa a da yanzu sun koma bayan Bukola Saraki

- Jiya kuma aka dakatar da wani ‘Dan-a-mutun Buhari bayan wasu 2 sun rasu

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya tarwatsa wadanda ke tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Majalisar. Wasu dai da ke tare da Shugaban kasar yanzu sun ja jiki sun koma bayan Bukola Saraki.

Bukola Saraki ya tarwatsa Sanatocin da ke tare da Shugaban kasa Buhari

Shugaba Buhari ya koma hannu-rabbana a Majalisar Dattawa

Idan ba ku manta ba kwanakin baya ne wasu Sanatoci irin su Sanata Abdullahi, Abu Ibrahim, Umaru Kurfi, Ali Ndume, Abubakar Yusuf, da su Omo-Agege su ka bayyana kan su a matsayin wadanda ke tare da Shugaban kasa a Majalisa.

KU KARANTA: An dakatar da Sanatan da ke tare da Buhari a Majalisa

Wani Sanatan APC daga Sokoto ya nemi a rusa wannan Kungiya da aka kafa cikin Majalisa kuma a hukunta Shugabannin ta. Shi ma dai Sanata Kabiru Marafa yace bai kamata a samu wasu Sanatoci da ke nuna mubaya’ar su ga Buhari ba.

Nan-take dai Shugaban Majalisar watau Bukola Saraki yace ka da ya sake jin wata Kungiya a Majalisar kuma ya nemi a janye karan da ke Kotu. Dama dai cikin kwanakin nan wasu Sanatoci 2 da ke tare da Shugaban kasa Buhari su ka rasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel