Kotu ta fitar da ranar ci gaba da zama kan batun Patience Jonathan

Kotu ta fitar da ranar ci gaba da zama kan batun Patience Jonathan

A ranar Alhamis din da ta gabata ne babbar Kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja, ta kayyade ranar 30 ga watan Afrilu domin ci gaba da gudanar da shari'ar Patience Jonathan, matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kotun za ta ci gaba da gudanar da shari'ar ne dangane da korafin kwace wasu manyan kadarori biyu mallakin matar tsohon shugban kasa domin maishe zuwa ga gwamnatin tarayya.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari ka iya jefa uwargidan tsohon shugaban kasar cikin tsaka mai wuya sakamakon rashin sanin hukuncin da shari'ar kotu za ta zartar kan wannan manyan kadarori da ta mallaka.

Patience Jonathan

Patience Jonathan

Hukumar hana rashawa da yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ita ce ke da alhakin wannan korafi da ta shigar tun a ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata.

KARANTA KUMA: 'Yan uwan Nnamdi Kanu sun buƙaci gawar sa domin binne ta

Hukumar ta bukaci kotun ta kwace gida wasu manyan kadarori biyu dake yankin Cadastral Zone a babban birnin kasar nan na tarayya sakamakon mallakar su ta hanyar rashin gaskiya da cin amana.

Mista Benjamin Mangi, shine lauya na bangaren hukumar EFCC mai rokon kotu da ta kwace wannan kadarori sakamakon bincike dake ci gaba da wakana a gare su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel