An tsinci gawar kananan yara 2 cikin Firinji a jihar Ondo

An tsinci gawar kananan yara 2 cikin Firinji a jihar Ondo

Mun samu rahoton cewa ibtila'i ya afkawa wata mahaifiya Misis Olubunmi Olaitan, yayin da ta yi kacibus da gawar 'ya'yayen ta biyu cikin Firinji a gidan su mai lamba ta shidda a unguwar Eyin Ala ta birnin Akure na jihar Ondo.

Legit.ng da sanadin jaridar The Punch ta ruwaito cewa mahaifiyar wannan yara, Olufemitan dan shekara 9 da kuma Oluwafifunmi dan shekara 7, ta gamu da mugun gani yayin da ta tsinci gawar 'ya'yan ta maza daskare a cikin Firinji.

An tsinci gawar kananan yara 2 cikin Firinji a jihar Ondo

An tsinci gawar kananan yara 2 cikin Firinji a jihar Ondo

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari ya afku ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin da Misis Olubunmi ta fita ta bar yaran na ta biyu suna wasanni inda dawowar ta ke da wuya ta yi kacibus da mugun gani.

KARANTA KUMA: Ta bayyana karara yadda aka kashe Zainab Alizee da diyar ta

Kakakin 'yan sanda na jihar Mista Femi Joseph, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari na kaddara mai ban tausayi.

Mista Femi ya yi bayanin cewa, ba bu wata alama da ta ke nuna kashe yaran aka yi, sai dai ya yi hasashen cewa ta yiwu kiriniya irin ta yara ta sanya wasa ya kai su ga shiga cikin Firinjin kuma suka gaza budewa yayin da murfin sa ya rufe da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel