Tashin hankali: Kotun duniya ta kasa-da-kasa na ta soma binciken Buhari kan laifuka 8

Tashin hankali: Kotun duniya ta kasa-da-kasa na ta soma binciken Buhari kan laifuka 8

Hankula suna ci gaba da tashi musamman ma a tsakanin manyan jami'an gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari sakamakon binciken da babbar kotun duniya ta kasa-da-kasa ta soma yi bisa laifuka har 8.

Mun samu wannan labarin ne dai a ta bakin babban ministan shari'a na gwamnatin Abubakar Malami wanda ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin sabon shugaban kotun ta duniya Farfesa Chile Osuji a ofishin sa garin Abuja.

Tashin hankali: Kotun duniya ta kasa-da-kasa na ta soma binciken Buhari kan laifuka 8

Tashin hankali: Kotun duniya ta kasa-da-kasa na ta soma binciken Buhari kan laifuka 8

KU KARANTA: An yi musayar zafafan kalamai tsakanin Amurka da Rasha

Legit.ng ta samu cewa haka ma Ministan Abubakar Malami ya bayyana cewa laifukan da ake zargin kasar da tafkawa sun hada ne da na rikicin Boko Haram da kuma tsakanin sojin Najeriya.

A wani labarin kuma, Jami’an hukumar nan ta gwamnatin tarayyar Najeriya da ke da alhakin hana fasa-kwauri wadda aka fi sani da Kwastam sun kai wani samamen ba-zata zuwa gidan gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal tare da kwace wasu motoci kimanin 160 da hukumar ke zargin an shigo da su ne ba bisa ka’ida ba.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, jami'an na Kwastam sun kai samamen ne a ranar jiya da dare wanda kuma ake sa ran hukumar za ta kira taron manema labarai dangane da wannan lamarin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel