Tafiya Landan: Jam'iyyar PDP ta bukaci majalisar tarayya da ta tsige shugaba Buhari

Tafiya Landan: Jam'iyyar PDP ta bukaci majalisar tarayya da ta tsige shugaba Buhari

Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya ta yi kira ga 'yan majalisar tarayyar kasar nan da su gaggauta kwace kambun shugaba Buhari tare da nada mataimakin sa a matsayin shugaban kasa biyo bayan tafiyar da yayi zuwa birnin Landan.

Wannan dai matakin dai a cewar jam'iyyar ya zama dole ne domin kare kasar nan daga shiga halin cakwakiyar shugabancin musamman ma dai ganin cewa shugaba Buhari din bai rubutwa majalisar ba kafin barin sa kasar.

Tafiya Landan: Jam'iyyar PDP ta bukaci majalisar tarayya da ta tsige shugaba Buhari

Tafiya Landan: Jam'iyyar PDP ta bukaci majalisar tarayya da ta tsige shugaba Buhari

KU KARANTA: Hukumar kwastam ta kai samame gidan Gwamna Tambuwal

Legit.ng ta samu cewa wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in yada labaran jam'iyyar Mista Kola Ologbondiyan ya fitar dauke da sa hannun sa.

A wani labarin kuma, Majalisar dattijan Najeriya a karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki ta amince tare da tabbatar da sabbin nade-naden da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na wasu mambobin hukumar nan ta cigaban yankin Neja Delta watau Niger Delta Development Commission a turance.

Wadanda aka amince da su din dai sun hada da Mista Chuka Ama Nwauwa daga jihar Imo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa daga jihar Ondo State sai kuma Nwogu N. Nwogu daga jihar Abia State.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel