Ba kanta: Hukumar kwastam ta kai samame gidan Gwamna Tambuwal, ta kwace motoci 160

Ba kanta: Hukumar kwastam ta kai samame gidan Gwamna Tambuwal, ta kwace motoci 160

Jami’an hukumar nan ta gwamnatin tarayyar Najeriya da ke da alhakin hana fasa-kwauri wadda aka fi sani da Kwastam sun kai wani samamen ba-zata zuwa gidan gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal tare da kwace wasu motoci kimanin 160 da hukumar ke zargin an shigo da su ne ba bisa ka’ida ba.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, jami'an na Kwastam sun kai samamen ne a ranar jiya da dare wanda kuma ake sa ran hukumar za ta kira taron manema labarai dangane da wannan lamarin.

Ba kanta: Hukumar kwastam ta kai samame gidan Gwamna Tambuwal, ta kwace motoci 160

Ba kanta: Hukumar kwastam ta kai samame gidan Gwamna Tambuwal, ta kwace motoci 160

KU KARANTA: Yan arewa sun ciwo gasar muhawara a kasar Singafo

Legit.ng dai ta samu cewa ana zargin gwamnan ya siyo motocin ne da nufin yin anfani da su wajen yakin neman zabensa a wa’adi na biyu na shekarar 2019 mai zuwa.

A wani labarin kuma, Hankula suna ci gaba da tashi musamman ma a tsakanin manyan jami'an gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari sakamakon binciken da babbar kotun duniya ta kasa-da-kasa ta soma yi bisa laifuka har 8.

Mun samu wannan labarin ne dai a ta bakin babban ministan shari'a na gwamnatin Abubakar Malami wanda ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin sabon shugaban kotun ta duniya Farfesa Chile Osuji a ofishin sa garin Abuja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel