Wata sabuwa: Hukumar 'yan sanda ta aikewa Sanatan Shehu Sani sammaci bisa zargin kisa

Wata sabuwa: Hukumar 'yan sanda ta aikewa Sanatan Shehu Sani sammaci bisa zargin kisa

Hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna ta aike da sammaci ga Sanata Shehu Sani domin amsa tambayoyi a kan zargin hannunsa a aikata wani kisan kai.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Austin Iwar, ne ya rubuta wasika zuwa ga Sanatan yana mai bukatar sa da ya bayyana a ofishin hukumar na jihar Kaduna nan da ranar 30 ga wata domin amsa tambayoyi.

"Muna gayyatar ka dangane da wani laifin kisan kai da hukumar soji, runduna ta 1 dake nan Kaduna ta aiko mana tare da wani faifan murya na CD da aka ambaci sunanka a matsayin babban wanda ake zargi," a cewar Iwar, cikin wasikar da ya aikewa Sanata Shehu Sani.

Wata sabuwa: Hukumar 'yan sanda ta aikewa Sanatan Shehu Sani sammaci bisa zargin kisa

Sanatan Shehu Sani

Jaridar premium times ta ce ta samu kwafi na wasikar a yau, Alhamis.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce aike da wasikar ya zama tilas domin hukumar na son yin adalci a binciken ta. An aika wasikar ga Sanata Shehu Sani ta hannun magatakardar majalisar dattijai. Kazalika an aike da kwafi ga shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Majalisar wakilai ta aikewa Osinbajo sammaci, zata yi masa titsiya a kan wani mataki da ya dauka

Ya zuwa yanzu babu rahoton cewar Sanata Sani ya furta wani kalami dangane da wasikar.

Kazalika hukumar 'yan sanda bata bayar da cikakken bayani a kan laifin kisan da take zargin hannun Sanatan ciki ba.

An dade ana tafka rikicin siyasa tsakanin Sanatan na Kaduna ta tsakiya da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Elrufa'i.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel