Dambarwar siyasa: Saraki ya roki kotun kuli ta kori karar da Gwamnatin tarayya ta kai shi

Dambarwar siyasa: Saraki ya roki kotun kuli ta kori karar da Gwamnatin tarayya ta kai shi

- Kotun koli ta soke tuhuma 15 daga cikin 18 da akewa Saraki

- Amma lauyan EFCC ya kekasa kasa yace, tabbas sarakin bai kamata a yafe masa tuhumar ba

Shugaban majalisar dattijai ta kasa Abubakar Bukola Saraki, ya roki kotin koli da ta kori karar da gwamnatin tarayya ta shigar tana zargin shi da laifuka har 18 akan zarginsa da rashin bayyana kadarorinsa ga kotun da’ar ma’aikata (CCT).

Dambarwar siyasa: Saraki ya roki kotun kuli ta kori karar da Gwamnatin tarayya ta kai shi

Dambarwar siyasa: Saraki ya roki kotun kuli ta kori karar da Gwamnatin tarayya ta kai shi

Shugaban majalisar ya bukaci kotun da ta taimaka ta kori karar ne a jiya yayin wani zama da kotun tayi, a cewarsa, gwamnatin tarayyar ta gaza samar da gamsassun hujjojin da zasu tabbatar da zargin da ake yi masa a kotun da’ar ma’aikata (CCT).

Sarakin ya ambata hakan ne, a yayin wani zama da kotun ta gudanar, inda yace, laifukan da ake tuhumar tasa da su anyi sune a wani yanayi mai kama da bita da kulli, domin har yanzu kotun da’ar ma’aikatar da doka ta baiwa ikon bincikawa da tabbatar da laifin ta kasa bincikawa yadda ya kamata har yanzu.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta kashe Biliyan 13 a kan yasar tashar ruwa

Babban lauya mai lambar kwarewa Kamu Agabi (SAN) ne, ya wakilci shugaban majalisar a kotun, ya kuma ce, maimakon CCT ta binciki Saraki kamar yadda doka ta tanadar, ta gaza hakan, sai dai kawai ta dogara ne da wani rahoto da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta fitar da shi suke amfani.

A cewar lauyan, kotun da’ar ma’aikatan tayi dai-dai da ta yanke hukuncin korar karar, saboda rahoton na EFCC ya saba doka. A saboda haka ne, lauyan yayi kira ga kotun da ta yi amfani da jawabin shaidar da wandanda gwamnatin tarayyar da kira don bayar da shaida, inda shaidun suka tabbatar da cewa basu da masaniyar laifukan da ake cajin Sarakin da su, a saboda haka kenan babu wani bincike da CCT ta gudananr akan sarakin.

Dambarwar siyasa: Saraki ya roki kotun kuli ta kori karar da Gwamnatin tarayya ta kai shi

Dambarwar siyasa: Saraki ya roki kotun kuli ta kori karar da Gwamnatin tarayya ta kai shi

Amma duk da haka lauyan gwamnati mai kwarewa da lambar girma Rotimi Jacobs (SAN), ya roki kotun da ta cigaba da sauraron karar, sarakin ya cigaba da zuwa kotun domin yana da laifin da ake kararsa da shi. A cewar Rotimi, babu wata doka da ta ce lallai sai an gudanar da bincike kafin a zargi mutum ya aikata laifi.

Ana shi bangaren kuwa mai shari’a Musa Mohammed Dattijo, ya dage sauraron karar har sai nan da 6 ga watan Yuli na 2018.

Bukola Saraki dai an kai shi kara kotun da’ar ma’aikata a shekarar 2015, bayan da ya zama shugaban majalisar dattijai.

Inda bayan jerengiyar zaman kotun da’ar ma’aikatan karkashin mai shari’a Dalladi Yukubu Umar, ya kori karar gami da wanke Sarakin, a dalilin rashin bin ka’idodin shigar da kara da masu karar suka yi.

Haka zalika bayan gwamnatin tarayyar ta daukaka kara zuwa kotun kolin ne, kotun ta kori laifuka 15 daga cikin 18 da gwamnatin take zargin Sarakin da su.

Dambarwar siyasa: Saraki ya roki kotun kuli ta kori karar da Gwamnatin tarayya ta kai shi

Dambarwar siyasa: Saraki ya roki kotun kuli ta kori karar da Gwamnatin tarayya ta kai shi

Kutun daukaka karar dai ta yanke hukuncin korar laifuka 15 da ake tuhumarsa da su ne, a wani zama da tayi ranar 12 ga watan Disambar shekarar da ta gabata, sannan kotun ta ce Sarakin ya cigaba da kare kansa daga sauran laifuka ukun da ake tuhumarsa.

Sakamakon korar laifuka 15 da ake tuhumarsa da kotun tayi ne, ya sanya yanzu Sarakin yake rokon kotun da ta sake dubawa sosai ta kori ragowar laifuka ukun da suka rage.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel