Da duminsa: Majalisar wakilai ta aikewa Osinbajo sammaci, zata yi masa titsiya a kan wani mataki da ya dauka

Da duminsa: Majalisar wakilai ta aikewa Osinbajo sammaci, zata yi masa titsiya a kan wani mataki da ya dauka

Kwamitin Majalisar wakilai a mai kula da ma'aikatar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ya aikewa da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo sammaci.

Kwamitin ya aikewa Osinbajo sammacin domin ya bayyana gabansa ya yi bayanin dalilan da suka saka shi dakatar da wasu darektocin hukumar ba bisa ka'ida ba.

Kwamitin ya aike da sammacin ne a yau, Alhamis, yayin zamansa da yake yi domin binciken badakalar cin amanar jama'a a hukumar.

Da duminsa: Majalisar wakilai ta aikewa Osinbajo sammaci, zata yi masa titsiya a kan wani mataki da ya dauka

Osinbajo da Dogara

Kwamitin na zargin Osinbajo da dakatar da darektocin ba bisa ka'ida ba, sannan a yayin da kwamitin majalisar ke binciken badakala a hukumar.

DUBA WANNAN: An yankewa alkalin kotun Najeriya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari

A cikin wadanda aka aikewa da sammacin bayan Osinbajo, akwai shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu da kuma shugabar hukumar kula da aikin gwamnati, uwargida Winifred Oyo-Ita.

Kwamitin na bukatar su da su bayyana domin bayanin irin rawar da suka taka wajen dakatar da darektocin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel