Kasar Saudiyya ta gudanar da bikin nuna kwalliyar mata a karo na farko

Kasar Saudiyya ta gudanar da bikin nuna kwalliyar mata a karo na farko

A karo na farko a tarihin kasar Saudiyya, an fara gudanar da bikin nuna kwalliya da kwalisar mata a babban birnin kasar, Riyadh wanda za'a kwashe mako guda daya gudanarwa.

Mata masu launin fata daban-daban daga kasar Saudiyya da kasashen gabashin Turai ne suka cika dakin da ake taron nuna kwalliyar da kwalisa.

Fitattun 'yan kwalisa da kwararrun masu iya kwalliya daga Turai sun nuna matukar mamakinsu da jin dadi bisa halartar taro irin wannan a kasar Saudiyya.

Kasar Saudiyya ta gudanar da bikin nuna kwalliyar mata a karo na farko

Kasar Saudiyya ta gudanar da bikin nuna kwalliyar mata a karo na farko

An sassauta tsauraran akidun Islama a Otal din Ritz-Carlton inda bikin ke gudana.

DUBA WANNAN: Ta rinchabe a Majalisa yayinda Sanatan PDP yace shugaba Buhari ya gaza

Kasar Saudiyya, karkashin sabon yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, na kawo canje-canje a yanayin tafiyar da harkokin rayuwar kasa da a baya ke biyayya ga tsarin addinin Islama.

A dalilin canje-canjen mata a wasu biranen kasar Saudiyya sun fara sanya hijabi masu launuka daban-daban,wasu lokutan ma har ado da leshi akeyi hijabin ko kuma a bar dan tsagu inda har za'a iya ganin dogon skirt ko wando samfurin jeans.

Direktan shirya bukin nuna kwalliyar, Layla Issa Abouzeid tace ana sa ran mutane 1500 ne zasu hallarci bukin kuma 400 daga cikinsu zasu zo daga kasashen waje ne. Ta kuma ce tana fatan bukin zai janyo wa kasar kudaden shiga tare da karfafa basirar yan kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel