Gwamnoni ne ke haddasa kashe-kashen makiyaya – Shehu Sani

Gwamnoni ne ke haddasa kashe-kashen makiyaya – Shehu Sani

Shehu Sani, sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya yayi zargin cewa gwamnoni ne keda hakki akan yawan kashe-kashen da makiyaya keyi a wasu yankunan Najeriya.

Dan majalian ya bayyana hakan a shafinsa na twitter inda yace gwamnoni dake amfani da tsarin tura kudi kan yarjejeniya ne ke haddasa kashe-kashen makiyaya a kasar.

Sani ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi barazana ga wadannan gwamnoni kamar yadda kasar ke fuskantar barazanar tsaro.

Gwamnoni ne ke haddasa kashe-kashen makiyaya – Shehu Sani

Gwamnoni ne ke haddasa kashe-kashen makiyaya – Shehu Sani

Ya rubuta kamar haka: “Tushen kisan kiyashin da makiyaya keyi a yankunan Najeriya ya samu asali ne daga tsarin da wasu gwamnoni ke bi na biyan Makiyaya. Suna lallashin azzalumai da kudin jama’a sannan yanzu azzaluman na bin kofa-kofa.

KU KARANTA KUMA: Bin Salman ya wasa wuka don yakar Shuraim daya da cikin limaman Kaaba

“Duk Gwamnan jihar dake aiki da wannan tsari na tura kudade ga makiyaya masu kisa shine jigonsu. Ya kuma dole a kale shi kamar barsazana ga tsaron kasa.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel